Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitin farfado da shirin Haihuwa Lafiya

0 245

Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitin mai mambobi 23 da zai bayarda rahoton hanyoyin da za’a bi wajen ganin masu juna biyu sun sauka lafiya da nufin farfado da shirin a jihar.

Sakataren gwamnatin jiha nan, Bala Ibrahim ne ya kaddamar da kwamatin a ofishin sa, kamar yadda wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin Ismaila Ibrahim Dutse ya fitar.

Bala Ibrahim ya zayyana sharuddan kwamitin da suka hada da gudanar da nazari na fasaha da zai bayarda da damar haihuwa lafiya ga mata masu juna biyu.

Kwamatin kuma zai bayarda rahoton yadda za’a haɓaka tsarin yin hoto da kuma bayarda shawarwarin abinci mai gina jiki ga mata masu shayarwa. Hakanan kwamitin nada alhakin yadda za’a samarda motoci domin jigilar mata masu juna biyu a lokutan Nakuda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: