Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta yin amfani da lambobin gwamnati a motocin ma’aikata

0 345

Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta yin amfani da lambobin gwamnati a motocin maaikata da sauran alumma na kashin kansu.

Shugaban Hukumar tara kudaden shiga ta jiha, Nasiru Sabo Idris ya sanar da hakan ta cikin shirin Radio Jigawa na musamman.

Yace gwamnati ta bada umarnin dawo da lambobin gwamnati da aka amfani dasu a motocin mutane bana gwamnati ba cikin gaggawa.

Mallam Nasiru Sabo ya kara da cewar yin amfani da lambobin gwamnati a motocin da bana gwamnati be cin amanar kasa ce kuma hakan yana ragewa gwamnati samun kudaden shiga.

Shugaban hukumar tara kudaden shigar ta jiha, yace zasu rinka yin sintiri na musamman da sauran jamian tsaro domin kama motocin da suke dauke da lambobin gwamnati a motocin da bana gwamnati ba.

Yana mai cewar hukumar zata cigaba da wayar da kan mutane kan muhimmancin biyan kudaden shiga domin kara baiwa gwamnati damar aiwatar da Karin aiyuka daga kudaden shigar da take samu na cikin gida Mallam Nasiru Sabo daga nan ya shawarci masu motoci da suke amfani da lambobin gwamnati dasu hanzarta mayarwa hukuma ko kuma su gamu da fushin ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: