Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta sayar da man fetur a cikin jarkoki ko wani mazubi a fadin jihar

0 273

Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta sayar da man fetur a cikin jarkoki ko wani mazubi a fadin jihar.

Wannan na kunshe cikin wata dokar zartarwa wacce gwamnan jiha Muhammad Badaru Abubakar ya sanyawa hannu.

Dokar tace an hana dukkan gidajen mai da ke jihar sayar da man fetur sama da lita 60 a cikin kowane mazubi ko jarka, ga wani mutum guda, sai dai kamfanoni da hukumomi.

Ya kara da cewa duk masu tallar man fetur, ban da gidajen mai masu lasisi, an hana su ajiye fiye da lita 60 na mai a kowane lokaci.

Dokar ta ce matakin zai taimaka wa gwamnatin jihar a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar.

Sawaba Radio ta bayar da labarin cewa a baya gwamnatin jihar ta takaita zirga-zirgar babura daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: