Gwamnatin jihar Jigawa ta fito da wani shiri na amfani da fasaha wajen koyo da koyarwa a jihar

0 290

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta fito da wani shiri na amfani da fasaha wajen koyo da koyarwa don inganta harkar ilmi a jihar nan.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dr Isa Yusif Chamo ya sanar da hakan lokacin taro na kwanaki uku kan nazari kan koyo da sanin yadda ake amfani da sabuwar fasahar a Dutse.

Ya ce gwamnatin jihar ta fito da wani shiri shekaru biyu da suka gabata domin tabbatar da cewa koyarwar ta dace da zamani.

Dakta Isa Yusuf Chamo yana mai cewa gwamnatin tarayya ta fito da wannan tsari, inda jihar Jigawa ta ci gaba da aiwatar da shirin.

Ya ce ana horar da malamai 350 kuma za su koyar da wasu malamai a makarantunsu, yayin da ya bukaci malamai su mayar da hankali kan abin da za su koya domin amfanin makarantun jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: