Gwamnatin jihar Jigawa ta fara yashe gurbataccen ruwa a ramin Tumballe da ke karamar hukumar Malammadori

0 235

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara yashe gurbataccen ruwa a ramin Tumballe da ke karamar hukumar Malammadori.

Mashawarci na musamman ga gwamnan jihar kan shigar da al’umma cikin gwamnati, Hamza Muhammad Hadejia ya ce gwamnatin jihar ta yi alƙawarin rage yawan gurɓataccen ruwan da ya mamaye tafkin sakamakon ruwan sama.

Hamza Hadejia ya ce gwamnatin jihar Jigawa ta samar tare da kafa manyan injina guda biyu da man fetur don aikin kwashe ruwan.

Ya kara da cewa yashe ruwan akan lokacin zai rage barazanar ambaliyar ruwa a kan gidajen da ke kusa da ofishin ‘yan sanda da ofishin INEC da gine-ginen hukumar ilimi na karamar hukuma da kuma kotun shari’ar da ke makwabtaka da tafkin.

Idan za a iya tunawa, ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya mamaye tafkin a bara ya tumbatsa inda ya lalata gidaje da ke kusa da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: