Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a jihar

0 53

Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Jigawa, Muhammad K Dagaceri.

Ya ce tuni wasu ma’aikata suka samu albashin watan Disamba.

Ya yi kira ga ma’aikata a jihar da su maida hankali wajen sadaukar da kansu ga aikin da kuma mara wa gwamnati baya domin ci gaba da gudanar da kyakkyawar alakar aiki. Idan za a iya tunawa, Gwamna Umar A Namadi ya sanar da amincewa da biyan sabon mafi karancin albashi daga ranar 1 ga Disamba, 2024.

Leave a Reply

%d bloggers like this: