Gwamnatin jihar Jigawa ta fara aikin hakar kogin Hadejia

0 531

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta sayi injunan yashe magunan ruwa guda biyu sannan ta fara aikin hakar kogin Hadejia domin share magudanar ruwa.

An kaddamar da wannan ci gaban ne domin hana afkuwar ambaliyar ruwa a nan gaba, bayan da jihar ta fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a bara.

Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa, Yusuf Sani Babura ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da Sawaba kan ayyukan riga-kafin ambaliyar ruwa a jihar Jigawa.

Idan zamu iya tunawa dai kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a wani bincike a ranar 26 Yuni 2023, yayi cikakken bayani kan abin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na dakile ambaliyar ruwa tare da bayyana wasu kalubalen da mazauna yankunan ke fama da shi.

Da yake mayar da martani dangane da illar ambaliyar ruwa, Yusuf Sani Babura ya ce gwamnati na aiki ba dare ba rana domin hakar koguna. Yusuf Sani ya kuma zargi mazauna wasu garuruwa da kin yin ƙaura domin sauya matsugunni duk da tallafin kuɗin da gwamnatin jihar ke bayarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: