Gwamnatin jihar Jigawa ta ce hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa da tsaro ta kasa ta bayar da tallafi ga yan gudun hijira a jihar

0 162

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa da tsaro ta kasa (NIMASA) ta bayar da kayan aikin kanana da matsakaitan masana’antu ga ‘yan gudun hijira a jiharnan.

Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Adamu Abdulkadir Fanini ne ya bayyana haka yau a cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse.

Adamu Fanini ya ce kayan aikin da aka bayar sun hada da kekunan dinki, injin nika, injinan janareto, kayan kwalliya, babura, da sauran su.

Adamu Fanini, wanda ya jinjina wa hukumar bisa gudunmawar da ta bayar ga mutanen da suka rasa muhallansu, ya ce wakilin hukumar, Adamu Dankura ne ya gabatar da kayayyakin ga gwamnatin jihar.

Adamu Fanini ya sami wakilcin Babban Sakataren Gudanarwa da Kudi, Alhaji Muhammad Dagaceri, ya godewa hukumar bisa wannan karamci.

Adamu Fanini ya rawaito Adamu Dankura na cewa gudummawar ta kasance don jajantawa mutanen jiharnan da kuma kula da ‘Yan Gudun Hijira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: