Gwamnatin jihar Jigawa ta bukaci masu yin NYSC da su zauna a jihar

0 233

Jagorar hukumar matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) a jihar Jigawa, Hajiya Aishatu Adamu, ta shawarci masu yiwa kasa hidima da aka turo jiharnan su zauna a jihar.

Aishatu Adamu ta ba da shawarar yau a jawabin maraba da ta yi wajen kaddamar da bikin wasanni da al’adu na bana a Dutse.

Ta yi bayanin cewa jihar tana da hanyoyi da yawa wadanda masu yiwa kasa hidima za su iya amfani da su domin rayuwa.

Jagorar ta kara bayyana Jigawa a matsayin jiha daya tilo wacce ma’aikatu da hukumomin gwamnati ba sa kin karbar masu yi wa kasa hidima

A nasa jawabin, Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya yabawa hukumar NYSC saboda zabar jihar a matsayin wajen gudunar da bikin wasanni da al’adu.

Gwamna Badaru, wanda Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jiharnan, Alhaji Bala Ibrahim ya wakilta, ya bayyana shirin NYSC a matsayin mai nagarta wanda ke cigaba da habaka hadin kai da fahimtar juna tsakanin ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: