Gwamnatin jihar Jigawa na ci gaba da biyan hakkokin wadanda sukayi ritaya

0 112

An shiga rana ta biyu ta biyan hakkokin maaikata da suka yi ritaya daga aiki a pension House dake Birnin Dutse.

Rukunin maaikatan jiha da kananan hukumomi da kuma na sashen Ilmi da suka yi ritaya daga aiki kimanin 465 ne ake biyan hakkokin nasu bayan an tantance su.

A jawabin da ya gabatar kafin fara biyan hakkokin maaikatan a rana ta biyu, sakataren zartarwa na Hukumar asusun adashen gata na fansho da kuma kananan hukumomi Dr Bilyaminu Shitu Aminu ya ce gwamna Umar Namadi ne ya bada kudade domin biyan hakkokin maaikata domin tallafawa rayuwarsu da kuma ta iyalansu.

Ya kuma ce za a biya hakkokin maaikatan ne rukuni hudu da suka hadar da maaikatan da suka yi ritaya daga aiki su 465 da hakkokin maaikatan da suka rasu a bakin aiki su 103 da cikon kudaden fansho ga yan fansho 39 da suka rasu alhali basu cika shekaru biyar suna karbar fanshon ba da kuma maaikata biyu da za a mayarwa da kudaden asusun adashen gata da suka tara.

Dr Bilyaminu Shitu Aminu ya kuma yabawa gwamna Umar Namadi bisa kulawar da yake yiwa hukumar a kowane lokaci.

Leave a Reply