Gwamnatin jihar Edo ta kori malamai 13 na jami’ar Ambrose Ali Ekpoma mallakar jihar bisa laifukan da suka hada da karyar yawan shekaru, zamba, rashin da’a, karbar kudi da kuma cin zarafin dalibai mata da sauransu.
Mataimakin shugaban cibiyar, Farfesa Asomwan Sunny Adagbonyin, ya bayyana hakan a jiya.
A cewarsa, korar ma’aikatan da suka yi laifin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin ladabtarwa na jami’ar wanda ya same su da aikata laifukan.
An bada shawarar korar wani malami wanda shi ne shugaban sashen ilimin aikin jinya bayan an same shi da laifin cinye kudaden dalibai biyu na naira dubu 32 da naira dubu 52.
Mataimakin shugaban jami’ar ya kara da bayyana cewa an kori wani farfesa da wani malami daga aiki saboda karbar kudaden da ba a amince da su ba daga dalibai yayin da kuma aka kori wani malamin da aka tuhume shi da laifin cin zarafin daliba mace.