Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta fara kidayar mata masu zaman kansu na mako daya don taimaka musu su koyi sana’o’in dogaro da kai su bar harkar.
Kwamishinan Hukumar Hisbah ta Jihar Bauchi, Aminu Balarabe, ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da shirin tallafa wa mata masu zaman kansu a ranar Laraba a Bauchi.
Aminu Balarabe ya ce a karkashin shirin, gwamnatin jihar za ta taimaka wa masu son komawa wurin danginsu daga cikin matan.
Ya ce shirin ba shi da nufin cin zarafi ko nuna musu wariya, kuma gwamnatin jihar Bauchi ta fara shi ne bayan tattaunawa sosai da kuma la’akari da halin da karuwai ke ciki.
Hakan ne ya sa gwamnatin jihar shirya hanyoyi da kuma irin taimakon kudade da na tarbiya da matan suke bukata domin kyautata rayuwarsu.