Gwamnatin Jigawa Zata Yi Hobbasa Kan Matsalar Ambaliyar Ruwa

0 247

Gwamantin jihar Jigawa ta jadadda kudurinta na kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa dake addabar alummar jihar.

Mataimakin gwamnan jiha, Alhaji Umar Namadi, ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci wuraren da ambaliyar ruwa tayi ta`adi a rukunin gidaje na Malam Inuwa Dutse da kuma cikin garin Dan`masara a Dutse.

Yace makasudin ziyarar shine ya jajantawa mutanen da iftila`in ya rutsa dasu tare da duba yanayin ta`adin domin tantancewa.

Alhaji Umar Namadi ya bayyana damuwa dangane da yadda ambaliyar ruwan tayi barna a wuraren da ya ziyarta, inda ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jiha ta tantance yanayin ta`adin domin basu tallafin gaggawa.

Haka kuma yayi addu`ar Allah ya kare afkuwar ambaliyar a nan gaba.

Wasu daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa sun nuna damuwarsu bisa yadda ambaliyar ta rushe musu gidaje da lalata dukiyarsu.

Daga nan sun yi kira ga gwamnatin jiha da masu hannu da shuni su kawo musu dauki domin rage musu wahalhalun da suke fuskanta.

Mataimakin gwamnan na tare da dan`majalisar dokokin jiha mai wakiltar karamar hukumar Dutse, Alhaji Musa Sule, da kuma sakataren zartarwa na hukumar bada agajin gaggawa ta jiha, Alhaji Yusuf Sani Babura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: