Gwamnatin Jigawa za ta mayar da dalibai 184 dake karatu a Sudan zuwa wasu jami’oin a kasashen Turkiyya da Cyprus

0 371

Majalisar zartaswar jihar jigawa a zaman na jiya, ta amince da sama da kudade naira biliyan 1.7 a matsayin kudin makaranta ga dalibai 184 dake karatu a Sudan wanda aka za’a mayar wasu jami’oi a kasashen Turkiyya da Cyprus.

Kwamashinan ilimi matakin farko na jiha Dr. Lawan Yusuf Dan zomo, ya bayyana haka ga manema labarai bayan zaman majalisar wanda gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse.

Danzomo yayi bayanin cewa daliban 100 da suka hada da maza da mata gwamnatin data gabata ce da hadin guiwa da gidauniyar Indimi suka dauki nauyin karatunsu domin karanta likitanci da sauran fannoni daban-daban.

Kwamshinan ya kuma kara da cewa, gwamnatin jiha ta kammala dukkan shirye-shirye ga daliban domin cigaba da karatunsu a kasar Turkiyya. Haka kuma majalisar zartaswar ta amince da gyaran wasu makarantun sakadiren kwana 14 da suka lalace sanadiyyar iska da ruwan sama, inda aka ware sama da naira miliyan 360.

Leave a Reply

%d bloggers like this: