Gwamnatin Jigawa ta zuba jarin sama da Naira Biliyan 5 a ayyukan tallafawa manoma

0 226

Gwamnatin Mallam Umar Namadi ta ce ta zuba jarin sama da Naira biliyan 5 a ayyukan tallafawa manoma domin karfafa samar da abinci.

Namadi ya bayyana haka ne a Dutse a jawabin da ya gabatar na bikin cika shekara guda na mulkin sa.

Ya ce gwamnati ta zuba Naira biliyan 5 ga kamfanin samar da ayyukan noma na jihar Jigawa, domin samar da kayayyakin amfanin gona a kan lokaci.

Namadi ya ce gwamnati ta bullo da wata manufofi masu nagarta kan harkokin noma, don daidaita ayyukan noma da samar da abinci a jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: