Gwamnatin Jigawa ta ware Naira miliyan 413 domin dakile matsalar tsaro a jihar

0 84

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce an ware zunzurutun kudi har naira miliyan 413 domin siyan babura 50 da motoci hudu a ci gaba da kokarinta na dakile matsalar rashin tsaro a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu, Sagir Musa ya sanyawa hannu a ranar Talata, majalisar zartaswar jihar karkashin jagorancin gwamna Umar Namadi, ta amince da sayan ne domin bunkasa sintiri da yaki da miyagun laifuka a jihar.

Musa ya ce majalisar ta kuma amince da Naira miliyan 304 don siyan motoci bakwai na jami’ai da na ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare don tabbatar da sa ido da tantance ayyukan ma’aikatar.

A cewar sa, majalisar ta kuma amince da aiwatar da wasu muhimman shawarwari daga kwamitin binciken fashewar tankar mai na Majia domin kaucewa afkuwar irin wadannan munanan al’amura a jihar nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: