Gwamnatin Jigawa ta ware ₦1,510,316,180 domin biyan mutanen da ayyukan tituna suka shafa a jihar

0 38

Majalisar zartaswa ta Jihar Jigawa ta amince kudi da ya kai Naira ɗaya da miliyan ɗari biyar da goma da dubu ɗari uku da sha shida da Naira ɗari da tamanin domin biyan diyya ga mutanen da ayyukan tituna suka shafa.

Wadannan ayyukan sun hada da titin Fagam zuwa Kila zuwa Jugwa zuwa Sakuwa a yankin Gwaram da Sankara a Ringim, da Bulangu a Kafin Hausa, da Gandun Sarki a karamar hakumar Malam Madori, da Dansure a Roni, da Aujara a Jahun, da wasu sassa na karamar hukumar Dutse.

Gwamnatin ta ce wannan kuduri na cikin kokarinta na inganta ababen more rayuwa da kuma tallafa wa al’umma da suka rasa muhallansu sakamakon ayyukan raya kasa.

Ana sa ran wannan mataki zai kawo sauki ga mutanen da ayyukan suka shafa tare da inganta harkokin sufuri a yankunan.  

A watan satumbar bara ne dai gwamnatin jigawa ta amince da gina tituna 45 masu nisan kilomita 835 akan kudi naira biliyan 300, domin ingantar harkokin sufuri da zirga-zirge a fadin jiha.

Leave a Reply