Gwamnatin Jigawa ta Sayo Na’urorin Gwajin Coronairus Na Miliyoyin Naira

0 308

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin da ya kai ziyara zuwa cibiyar kebe wadanda ka iya kamuwa da cutar a Dutse, a Otal din three star da kuma sansanin horas da masu yiwa kasa hidima da ke Fanisau.

Kwamishinan lafiya na jiha kuma shugaban Kwamatin karta kwana kan cutar Covid-19 Dakta Abba Zakari ne ya kewaya da da gwamna Muhammad Badaru Abubakar a cibiyar.

Bayan kammala duba cibiyar ne gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya nuna gamsuwa bisa shirin da ‘yan kwamitin karta kwana kan cutar suke yi.

Haka zalika gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya gudanar da taro da wakilan kwamitin, inda ya bukaci al’umma su kara kiyayewa da ka’idojin da likitoci suka bayar tare da yin addu’oin neman kariya daga Allah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: