Gwamnatin Jihar Jigawa ta rabawa manoma 50 ingantaccen irin shuka dan Brazil domin nomawa a gona mai fadin kadada 80 a wannan damina.
Mai bawa Gwamna shawara kan noman shinkafa, Alhaji Jamilu Dan-Mallam ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta masu ruwa da tsaki a aikin gona zuwa wasu fadamu dake kananan hukumomin Dutse da Hadejia da Kazaure.
- Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi bane – Gwamnatin Tarayya
- Aƙalla ‘yan ƙasar Nijar 300 ne ake zargin hukumomin Libiya sun tsare
- Mutum 7 sun mutu yayin zanga-zangar bayan zaɓe a Mozambique
- Da yiwuwar Amurka ta fitar da hannunta daga yaƙe-yaƙen ƙasashen ƙetare
- Ƙungiyar dillalan man fetur ta cimma matsaya da Dangote kan sayen man fetur
Alhaji Jamilu Dan-Mallam ya shawarci manoman da aka rabawa irin, da su tabbatar sun cika alkawuran da suka dauka na dawo da rancen iri ko kudaden da aka basu domin wasu manoman su amfana.
A nasa jawabin, mukaddashin Manajan Daraktan hukumar bunkasa aikin gona da raya karkara ta jiha, JARDA, Alhaji Bashir Mu’azu Majiya ya yi kira ga manoman da su rika aiki da shawarwarin malaman gona domin bunkasa nomansu.