Gwamnatin Jigawa ta kafa wani sabon kwamiti domin kula da Asibitin Gwamnati na Dutse

0 161

Shugaban kwamitin shi ne Daraktan Lafiyar Jama’a, Dakta Mahmud AbdulWahab. Kwamitin ya kunshi daraktoci daga Ma’aikatar Lafiya da kuma wakili daga fadar Sarkin Dutse.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Muhammad Abdullahi Kainuwa, ne ya kaddamar da kwamitin a ofishinsa. Ya bayyana cewa an dauki matakin ne sakamakon wasu matsaloli da aka gano a cikin ayyukan asibitin. Kwamishinan ya gargadi ma’aikatan cewa gwamnati ba za ta lamunci sakaci ba, musamman ganin irin kudaden da ake kashewa a bangaren lafiya.

Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya, Dakta Kabiru Ibrahim, ya bayyana cewa an ba wa kwamitin wa’adin watanni uku don kammala aikinsu. Daga cikin ayyukansu akwai tabbatar da da’a tsakanin ma’aikata, tsaftace asibitin, da kuma gano hanyoyin samun kudaden shiga ta hanyar harkokin kasuwanci da ke kusa da asibitin.
Shugaban kwamitin kuma mukaddashin mai kula da asibitin, Dakta Mahmud AbdulWahab, ya sha alwashin yin iya kokarinsu. Ya ce za su yi aiki tukuru don su cika burin da gwamnati ke da shi a kansu.

Taron kaddamar da kwamitin ya samu halartar shugabannin hukumomin lafiya, masu ba da shawara na musamman, daraktoci da ma’aikatan ma’aikatar lafiya.

Leave a Reply