Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da Daftarin Bunƙasa Noma mai nisan zango, na 2024 Zuwa 2030

0 195

A ƙoƙarin da Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ke yi domin bunƙasa harkokin noma da samar da abinci da aikin yi ta hanyar noma, ya fito da Daftarin Shirin Bunƙasa Noma na Shekarun 2024 Zuwa 2030.

Cikin wata sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Hamisu Gumel ya fitar wa manema labarai, ya ce an gudanar da bikin ƙaddamar da Daftarin Bunƙasa Noma a Dakin Taron Majalisar Zartaswa na Gidan Gwamnatin Jigawa.

Taron dai ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da wakilai daga Ofishin Bunƙasa Ƙasashen Rainon Ingila, wato Foreign, Commonwealth Development Office (FCDO) da kuma Procom+.

Gwamna Namadi ya jaddada cewa wannan sabon tsarin shirin bunƙasa noma na zangon shekaru bakwai na daga cikin ajandojin sa 12, waɗanda ya shata domin maida Jigawa jihar da ke sahun gaba wajen ƙirƙirowa da samar da yalwar arziki.

Ya nuna matuƙar buƙatar faɗaɗa aikin noman rani ya hanyar samar da kayan noma na zamani, domin samun nasarar shirin sosai.

“Muna jin cewa akwai matuƙar buƙatar inganta tsarin noma domin ya zo daidai da tunanin da muke yi na samar da yalwar arziki a fannin noma,” cewar Gwamna Namadi.

Ya kuma gode wa FCDO saboda shigar ta kane-kane cikin ayyukan bunƙasa tattalin arziki da ci gaba daban-daban a Jihar Jigawa.

Shawaracin Musamman a Fannin Noma na Gwamna kuwa, Dakta Saifullahi Umar, ya ce wannan tsari mai dogon zango na 2024 zuwa 2030, zai samar da ayyukan yi sosai ga ɗimbin matasan jihar.

Ya ce Allah ya albarkaci Jigawa da al’umma kusan miliyan 8, waɗanda ya ce fiye da miliyan 3 duk matasa ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: