Gwamnatin Jigawa hadin guiwa da UNICEF sun amince da N500M domin samar da abinci mai gina jiki ga yara

0 251

Gwamnatin jihar Jigawa da hadin guiwa da asusun tallafawa kananan yar ana majalisar dinkin duniya UNICEF sun amince da naira miliyan 500 domin samar da abinci mai gina jiki ga yara.

Shugaban shirin samar da abinci mai gina jiki a Jigawa Saidu Umar ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan amince da matakin.

Yayi bayanin cewa majalisar zartarwa ta jiha ta amince da sakin naira miliyan 200 da 50 domin shirin samar da abicin ga yara karkashin shirin RUTF.

Saidu ya kara da cewa, karkashin yarjejeniyar, Asusun UNICEF zai cika ta ragowar kashi 50 na kudaden da ake bukata domin fara rabon a cibiyoyin lura da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

A cewar sa akalla yara sama da dubu 10 ne dake fama da matsalar abinci mai gina jiki zasu ci gajiyar shirin a fadin jiha.

A nasa martanin shugaban gamayyar kungiyar lura da abinci mai gina jiki ta jiha JICCON kwamaret Shuaibu Isah ya bayyana shirin a matsayin shirin ceto rayuka da dama. Ya godewa gamayyar UNICEF da gwamnatin jihar Jigawa bisa yunkurin na magance matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: