Gwamnati zata biya ₦1,001,000,600,000 a matsayin tallafin wutar lantarki

0 156

Gwamnatin tarayya zata biya naira triliyan 1 da miliyan dubu 600 a matsayin tallafin wutar lantarki ga kostomomi a wannan shekarar ta 2024, yayin da hakumar dake lura da wutar lantarki ta kasa ta kara yawan kudaden da zata rika karba daga kostomomi.

Shugaban hakumar Sunusi Garba wanda ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Abuja, ya cewa, gwamnatin tarayyar zata rika biyan naira miliyan dubu 120 a kowane wata a matsayin kudin tallafin wutar lantarki.

Garba, wanda ya bayyana haka cikin wata sabuwar sanarwa ga kamfanonin rarraba wutar lantarki 11, cewa ba zasu kara kudin lantarkin ba tinda gwamnatin tarayya ta amince ta biya tallafi.

Shugaban hakumar ya jaddada cewa sabbin tsare-tsaren biyan kudin lantarkin zasu cigaba da kasancewa a yadda suke tun na 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: