Gwamnatin tarayya tace nan gaba kadan zata baiwa kamfanonin jiragen saman kasar nan umarnin biyan diyya ga fasinjojin da basu samu tashi ba.
Ministan jiragen sama Festus Keyamo, shine ya bayyana haka yayinda ya gana da masu kamfanonin jiragen sama jiya a Abuja.
Kazalika,Keyamo ya bukaci kamfanonin jiragen sama da su samu hanyar sadarwa mai inganci tsakanin su da fasinjojin su.