Gwamnati za ta ƙara himma sosai wajen jaddada ‘yancin ‘yan jarida

0 248

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnati za ta ƙara himma sosai wajen jaddada ‘yancin ‘yan jarida.

Da ya ke jawabi lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Idris ya ce ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai babban ginshiƙi ne wajen samun nasarar dimokuraɗiyya.

Kan haka ne ya ce gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai.

Shugabannin ƙungiyar dai sun kai masa ziyarar ne a ranar Talata, 10 ga Oktoba, 2023.

Ministan ya bayyana manyan ƙalubalen da ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai ke fuskata, waɗanda ya ce sun haɗa da ‘yancin su, samun damar mallakar bayanai da kuma tsaron lafiya da rayukan su.

Ya ce NUJ ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗorewar dimokiraɗiyya.

Ya jaddada cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da gaske ta ke yi wajen kula da ‘yancin ‘yan jarida, tare da ƙoƙarin ganin sun riƙa gudanar da aikin su ba tare da tsangwama ko wani cikas ba.

A jawabin sa, Shugaban NUJ na ƙasa, Mista Chris Isiguzo, ya fayyace ƙalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta, waɗanda su ka haɗa da ‘yancin ‘yan jarida, damar ba su bayanai a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati, tsaron lafiya da rayukan su da kuma matsalolin na yau da kullum na tsadar rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: