Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na farfado da masaku da nufin bunkasa noman audug`a da samar da tufafi da kuma rage dogaro da kayan sakashen waje.
Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Doris Nkiruka Uzoka-Anite, ta ce hakan ya hada da samar da injina da fasahohin zamani ta yadda bangaren zai iya fitar da kayyayi zuwa ko’ina a fadin duniya.
A cewar minisatar aiki ya yi nisa wajen zawarcin masu zuba jari a bangaren domin cim ma wannan manufa.
Doris ta sanar a wani zauren tattaunawa da masu harkar auduga da ya gudana a Abuja cewa, farfado da masakun zai samar a ayyuka 200,000 a cikin shekaru biyu masu zuwa.
Ministar ta jaddada cewa hakan zai bunkasa samun kudade ga masu harkar dinki da zayyana da manoman aduka, baya ga samar da cigaba a bangaren samar da tufafi a cikin gida.