Gwamnati na sake duba albashin ma’aikatanta a wani mataki na dakile illar cire tallafin man fetur
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya baiwa ma’aikatan kasar nan tabbacin shirin gwamnati na sake duba albashin ma’aikatanta a wani mataki na dakile illar cire tallafin man fetur.
Akpabio ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, da ‘yan majalisar dokokin jihar, a ziyarar ban girma da suka kai masa.
Ya kuma kara da cewa cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi ne da nufin magance matsalar cin hanci da rashawa a bangaren man fetur, inda ya ce matakin shi ne mafarin yaki da cin hanci da rashawa a kasa.
Da yake jawabi tun da farko, gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, ya yabawa shugaban majalisar dattawa bisa nasarorin da ya samu a ofis a cikin wata daya da ya gabata.