Gwamnan Kebbi ya bada motocin shinkafa guda 3 don bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

0 42

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bai wa Kiristoci kyautar manyan motocin shinkafa guda uku don tallafawa bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Mataimakin gwamnan na musamman kan harkokin addinin Kirista, Samuel Audu Dabai, ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a Birnin Kebbi.

Dabai ya ce wannan gudunmuwar tana nuni da irin kulawar gwamnatin jihar ga al’ummar Kirista, domin tabbatar sun gudanar da bukukuwansu cikin jin dadi da walwala. Ya kara da cewa Kiristoci a jihar sun kammala shiri don bikin Kirsimeti, inda wasu ke komawa gida daga waje, yayin da wasu kuma ke shirye-shiryen tafiye-tafiye zuwa garuruwansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: