Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ya sha alwashin kawo karshen ‘Ya bingida a jihar

0 213

Gwamnan ya fadi haka ne a jiya laraba yayinda ya kai ziyara sansanin horas da ‘yan sinitiri, wanda gwamnatin sa ta kirkira domin kawar da ‘Yan bindiga a jihar.

Ya kuma jadadda kwarinb gwiwar da yake da shi na yaki da matsalar tsaro a jihar, inda ya bayyana bukatar hada kai domin tabbatar da zaman lafiya.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin arewa maso yamma dake fama da matsalolin ‘Yan bindiga, sauran jihohin sun hada da Kaduna, Sokoto, Katsina da Kebbi. Duk da irin kokarin da gwamnatoci da hukumomin tsaro keyi na magance matsalar tsaro, amma duk da haka ‘yan bindiga na cigaba da kai munanan hare-hare a yankunan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: