Gwamnan jihar Yobe ya yi kira da a gudanar da bincike don gano musabbabin jefo bama-bam a kauyen Buhari
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya yi kira da a gudanar da bincike don gano musabbabin jefo bama-bama daga jirgin sama da yayi sanadiyar rayuka a kauyen Buhari, karamar hukumar Yunusari a jihar Yobe.
An bayar da rahoton cewa akalla mutane 8 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin da wani jirgin sama ya jefo bama-bamai kan mutanen kauyen a jiya da safe.
Mai magana da yawun rundunar sojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet, ya nisanta rundunar daga faruwar lamarin.
A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai, Mamman Mohammed, Gwamnan ya yi ta’aziyya da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a lamarin.
Mai Mala Buni ya kuma bayar da tabbacin shirye-shiryen gwamnatinsa don yin aiki tare da dukkan jami’an tsaro don tabbatar da tsaron jihar.
A halin da ake ciki, gwamnan ya umarci asibitocin gwamnati da ke garuruwan Geidam da Damaturu da su bayar da magani kyauta ga wadanda suka samu raunuka sakamakon harin.