Gwamna mai mala buni na jihar Yobe ya amince daukar ma’aikatan lafiya na Ungozoma 158 da suka kammala karatu a kwalejin aikin lafiya da ungozoma dake Damaturu, a matsayin yunkuri na bunkasa ayyukan kiwon lafiya a jihar.
An bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gwamnan Mamman Mohammed ya fitar.
A cewar sanarwar, sabbin ma’aikatan lafiyar da gwamna ya dauka aikin sun kasance yan rukurin ajujuwa 2 suka kammala karatu a kwalejin.
Gwamnan ya bukaci sabbin ma’aikan da suyi aiki bisa gaskiya da jajircewa. Yayi kira ga sauran dalibai da suyui karatu da kyau kamar yadda gwamnatin ke zuba jari akan su.