Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba kujerun zama masu mazauni uku-uku guda dubu 73,800 ga makarantun jihar da ke kananan hukumomi 44.
Wannan wani bangare ne na kudurinsa na inganta ilimi biyo bayan kaddamar da Dokar Ta-Baci kan Ilimi, domin tabbatar da cewa kowane yaro a Kano ya samu ingantaccen ilimi.
A wajen cibikin rabon da aka gudanar a Cibiyar Kasuwanci ta Kano, Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin samar da kayan makaranta domin taimaka wa dalibai wajen mayar da hankali domin samun ilimi.
Gwamnan, ya kuma gode wa matasa sama da 11,000, masu sana’ar kafinta da walda, wadanda suka bayar da gudunmawa wajen kammala aikin a kan lokaci.
Har wa yau, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafa wa fikirar matasa da kuma karfafa musu.
Wannan na daga cikin alkawuran da Gwamna Yusuf ya dauka a yakin neman zaben 2023.