Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf Kabir ya kaddamar da rabon tallafin Naira 50,000 ga mata 4,800 da aka zabo guda 1 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin a gidan gwamnati da ke Kano a jiya Talata, gwamnan ya ce kudaden da suka kai Naira miliyan 260, za a raba su ne a duk wata ga sabbin dauka 4,800 har zuwa karshen wa’adin mulkinsa.
A cewarsa, an kirkiro shirin tallafin ne don taimakawa iyaye mata wajen fara kasuwanci domin rage nauyin iyali.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, tallafin an yi shi ne don biyan tukuici ga mata bisa gagarumin goyon bayan da suka bayar don samun nasararsa a zaben 2023.