Gwamnan Jihar Jigawa ya nemi ma’aikatun jihar da su cimma yarjejjeniyar da jihar ta kulla da Ofishin FCDO
Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya yi kira ga ma’aikatu da sassan gwamnatin jihar da su cimma yarjejjeniyar da jihar ta kulla da Ofishin Cigaban Kasashen Waje na Commonwealth, FCDO.
Gwamnan ya yi wannan kira ne ta bakin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Muhammad K. Dakaceri a lokacin zaman duba nasarorin da aka samu wanda aka gabatar jiya Talata a Sakatariyar Jiha da ke Dutse.
Dakaceri ya bayyana cewar gwamnatin yanzu ta shirya samar da cigaba mai dorewa, inda ya ce hada kai da FCDO zai saukaka hanyar samun cigaban da ake bukata.
Ya kara da cewa, Gwamna Namadi ba zai taba aminta da gazawa a aiki ba daga kowacce ma’aikata da kasa yin abun da ake bukata a lokutan da aka ware.
Shugaban ma’aikatan ya kuma tabbatar da samun goyon bayan gwamnati da na FCDO wajen ciyar da Jihar Jigawa ba.