Gwamnan jihar Jigawa ya bayyana damuwarsa kan yawan rashin zuwa aiki a tsakanin ma’aikatan jihar

0 345

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana damuwarsa kan yawan rashin zuwa aiki a tsakanin ma’aikatan jihar da suka hada da manyan sakatarori a ma’aikatu daban daban.

Ya bukaci ma’aikatan jihar akan su sauya dabiar rashin zuwa wuraren aiki da wuri domin cigaban jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ziyarar bazata da ya kai wasu ma’aikatun gwamnati da ke Dutse babban birnin jihar, inda gwamnan ya gana da manyan sakatarorin guda uku da babban akanta janar da kuma daraktoci kadan. Wani babban jami’i daga ofishin shugaban ma’aikata da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce gwamnan ya umurce su da su fara daukar sunayen ma’aikatan da basa zuwa wurin aiki da wuri.

Manema labarai sun rawaito cewa Gwamnan ya kasance a sakatariyar jihar ne tun da karfe 11:30 na safe. Ya kuma zagaya ma’aikatu da hukumomin da ke cikin harabar gidan, inda ya tsaya har zuwa tsakar rana, sai dai ya gano cewa ma’aikata kadan ne ke fitowa aiki wadanda galibin su masu aikin share-share ne da kuma kananan ma’aikata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: