Gwamnan Jihar Filato yayi Allah wadai da kisan mutane 50 da aka yi a jihar

0 90

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang, ya bayyana cewa hare-haren da ake kaiwa  jihar, inda aka kashe fiye da mutane 50 tare da raba dubban mutane da muhallansu cikin ‘yan makwannin nan, ba dai-dai ba ne, ana daukar nauyinsu ne kuma suna da alamar kisan kare dangi.

Hare-haren sun fi kamari a wasu al’ummomi da ke cikin Karamar Hukumar Bokkos a Arewa ta Tsakiya, inda mutane da dama suka rasa matsugunansu, kana aka lalata dukiyoyi da dama.

Gwamna Muftwang, cikin takaici da bacin rai, ya danganta wadannan hare-hare da wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda da bai bayyana ba. Ya ce hare-haren an kitsa su ne don a kawar da wasu al’umma gaba daya daga jihar.

Ya kara da cewa lamarin ya wuce rikicin noma da kiwo da ake danganta matsalar jihar da shi a baya, yana mai cewa akwai alamun ta’addanci cikin hare-haren da ake kaiwa yanzu.

Masana bincike sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake fuskanta a jihar Filato na da tushe a rikicin albarkatu tsakanin manoma da makiyaya, amma Gwamna Muftwang ya ce wannan sabon salo na rikici ya wuce hakan, domin fiye da al’ummomi 64 ne ‘yan bindiga suka mamaye suka kuma raba mazauna da gidajensu.

Leave a Reply