Gwamnan Jihar Filato ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomin jihar

0 120

Gwamnan Jihar Filato ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomin jihar Filato 15 a cikin 17 da ake da su a jihar.

Gwamnan Jihar Filato Barista Caleb Mufwang ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomin jihar Filato 15 a cikin 17 da ake da su a jihar a daren jiya Alhamis a gidan gwamnatin jihar dake garin Jos.

Da yake jawabi a wajen rantsuwar Gwamna Caleb ya taya sababbin shugabannin murnar nasarar zaɓen da suka samu.

Ya yaba wa hukumar zaɓen jihar kan yadda ta gudanar da zaɓen a kan gaskiya da adalci. Don haka, ya yi alqawarin baiwa zaɓaɓɓun shugabanni cikakken goyon baya da hadin kai wajen gudanar da ayyukan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: