Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya nada mataimaka 168 da membobin gudanarwa 104

0 295

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya nada mataimaka 168 da membobin gudanarwa 104 na hakumomi da ma’aikatu 15 dake jihar.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnati Bukar Tijjani wanda ya sanyawa hannu a safiyar yau.

Yace wadanda aka nada sun hada manyan masu bayar da shawara 9, da mataimaka na musamman 81, manyan mataimaka na musamman na 78.

Sakataren gwamnatin ya kuma lissafo wasu shugabannin hakumomi da ma’aikatu 15 da aka nada. A cewar sa anyi nadin ne bisa cancanta kuma bisa doka ta 208(2)d na kundin dokar kasa wanda ya bawa gwamna damar nada mataimaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: