Gwamnan Jigawa Yayi Alkawarin Samar da Kayan jin kai ga al’umma Saboda Korona

0 185

Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki alkawarin samar da kayayyakin jin kai ga al’ummar jihar nan, a yanayin da ake ciki na dokar takaita zirga zirga, bayan samun karuwar cutar COVID19 a jihohin da ke makotaka da ita.

Sanarwar hakan ta fito ta bakin gwamnan jihar Jihar nan Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, a yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki a dakin taro na Ahmadu Bello da ke Dutse.

Gwamnan yayi bayanin cewa a yayin da jihohin da ke makotaka da jihar nan da suka hada da Jihar Kano, Bauchi, da kuma Katsina suka samu bullar cutar, gwamnatin jihar nan zata kara tsaurara matakan rufe iyakokin ta.

Kazalika gwamnan ya ce za’a hukunta duk wanda aka kama da karya dokar takaita zirga zirga kamar yanda sabuwar dokar da shugaban kasa muhammadu Buhari ya sanyawa hannu ta tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: