Gwamnan CBN Emefiele ya bukaci a biya shi diyyar Naira miliyan 500 bisa zargin bata masa suna daga Gudaji Kazaure yayi

0 227

Gwamnan babban bankin kasa, CBN, Godwin Emefiele, ya bukaci a biya shi diyyar naira miliyan 500 bisa zargin bata masa suna daga Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalisar wakilai.

Gudaji Kazaure, mai wakiltar mazabar  Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi daga jihar Jigawa, ya yi ikirarin cewa sama da naira tiriliyan 89 na harajin kan sarki sun bata daga baitulmalin CBN.

Dan majalisar wanda ya yi ikirarin cewa shi ne sakataren kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa a kan kwatowa da kuma sasanta duk wasu kudaden harajin kan sarki, ya zargi Godwin Emefiele da hadin gwiwar wasu jami’an gwamnati da kokarin dakile kokarin da kwamitin ke yi na kwato kudaden.

A wani martanin gaggawa, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya musanta zargin, yana mai cewa alkaluman da Gudaji Kazaure ya ambata, zatonsa ne kawai.

Sai dai a wata hira da ya yi da wani dan jaridar Muryar Amurka Nasir El-Hikaya a kafar Facebook, Gudaji Kazaure ya bayyana cewa gwamnan babban bankin na CBN ta bakin lauyansa ya bukaci ya janye zargin cikin kwanaki uku na aiki ko kuma ya fuskanci shari’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: