Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya tabbatar da sakin fursunoni 110 daga gidan yari na Kaduna, a wani bangare na shirye-shiryen bikin murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya 12 ga watan Yuni 2024.
Gwamnan tare da babban Lauyan Najeriya Femi Falana, sun ziyarci gidan gyaran hali a ranar Talata, inda ya ce matakin na daya daga cikin kokarin gwamnatinsa na rage cunkoso a gidajen yari da kuma baiwa fursunonin da suka cancanta dama ta biyu.
Ya ce a wasu lokuta, wasu daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin suna da tarar kudi da diyya, ko kuma wadanda aka fara shari’arsu amma har yanzu ana ci gaba da shari’a da sauransu yayin da wadanda aka yanke musu hukunci tarar ko zabin tarar su ma sun cika adadin.
Ya kuma kara da cewa, babu wata al’umma da za ta wanzu kuma ta dawwama ba tare da bin doka da oda ba, yana mai bayyana cewa, dole ne ‘yan kasa a kowane lokaci su nisanta kansu daga aikata laifuka tare da yin biyayya ga hukumomin da aka kafa.