Gwamna Namadi ya kaddamar da rabon kayan makaranta ga dalibai 30,000 a jihar Jigawa

0 367

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da rabon kayan makaranta ga dalibai 30,000 a manyan makarantun sakandire dake fadin jihar.

taron wanda ma’aikatar ilimi mai zurfi ta shirya wanda aka gudanar a makarantar sakandiren kimiyyar mata ta gwamnati da ke Jahun a karamar hukumar Jahun.

A nasa jawabin, Malam Umar Namadi ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko na musamman ga ilimin yara mata, don haka ne ake saye da rarraba kayan makaranta a kyauta ga yara mata.

A nata jawabin, shugabar kungiyar shugabannin makarantun sakandire (ANCOPSS), Hajiya Asmau Sulaiman, ta yabawa gwamnan kan wannan tallafin da kuma sa baki a harkokin ilimin yara mata a jihar.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Safiya Danladi da Zainab Ibrahim, sun yabawa gwamnati bisa wannan karamcin tare dayin alkawarin daukar karatunsu da muhimmanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: