Gwamna Namadi ya gargadi masu son karkatar da takin zamani da aka samar domin manoma

0 366

Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar kwamitin siyarwa da na rabon takin zamani, Tirela 200 na NPK domin manoman jihar.

Gwamnan ya kuma gargadi kwamitin da su ji tsoron Allah, tare da jan kunnen su kada su karkatar da takin.

Da yake jawabi yayin kaddamawar, Malam Umar Namdi yace gwamnatin jiha ce ta samar da takin,wanda ya kunshi Tirela 200 na NPK da buhuna 120,000 da za a siyarwa manoma bisa rangwame.

Kazalika, ya bukaci Mambobin kwamitin da su raba takin yadda ya kamata, bisa gaskiya da adalci ga Manoman.

Tunda farko Malam Namadi, yayin kaddamar da kwamitin takin a gidan gwamnati dake Dutse, ya bukaci mambobin kwamitin su ji tsoron Allah sannan su sauke nauyin dake kan su bisa gaskiya da adalci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: