Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yana ganawa a kasar Netherlands

0 289

Tawagar jihar Jigawa bisa jagoranci gwamna Muhammad Badaru Abubakar ta sauka a kasar Netherlands.

Tawagar ta samu tarba a filin jirgin saman Amsterdam daga jakadiyar Nigeria a kasar Netherlands Dr Eniola Ajayi da sauran manyan jamiai daga ofishin jakadancin da suka hadar da Oluremi Oliyide da Olufemi Olonijolu da kuma Maxwell Anu-Okeke.

A jawabinta na maraba ga tawagar a masaukin Nigeria dake Hague, jakadar Nigeria a Netherlands Ajayi ta yi musu fatan alheri a ziyarar da suka kai ta kwanaki bakwai.

Daga nan sai ta yi adduar samun nasarar ziyarar domin amfanin alummar jihar Jigawa da kuma Nigeria baki daya.

Tawagar ta kunshi kwamishinan aiyuka da sufuri Injiniya Aminu Usman Gumel da kwamishinan aikin gona Alhassan Muhammad da babban daraktan hukumar tantance aiyukan kwangila Alhaji Ado Hussaini da kuma jamiin lura da harkokin baki na gwamnan jiha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: