Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin sabon Daraktan Cibiyar Horas da Ma’aikata

0 243

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin Alhaji Umar Farouk Dutse a matsayin sabon Daraktan Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Jihar Jigawa dake Dutse wato Manpower.

Wanna na kunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini ya sanyawa hannu.

Alhaji Farouk Dutse, ya taba zama Mamba a hukumar gudanar da Cibiyar daga shekarar 2015 zuwa 2019.

Sanarwar ta taya Sabon Daraktan Cibiyar ta Manpower Development Institute Murna, bisa nadin da aka masa, tare da masa fatan gama aikin sa Lafiya.

Kazalika, sanarwar tace nadin nasa ya fara aikin nan take.

Leave a Reply

%d bloggers like this: