Gwamna Ganduje yayi kira ga al’ummar jihar Kano da su kwantar da hankalinsu kuma kar suna tada husuma

0 205

Gwamnan jihar kano Abdullahi Ganduje yayi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, tare da kauracewa dukwani nau’in ayyukan da zai iya kawo tsaiko akan zaman lafiyan a jihar.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar musamman matasa, da su hada kansu domin dabbaka zaman lafiya a jihar, musamman wajan hada kai da sauran

 kabilun jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin kwamishina yada labarai na jihar Muhammad garba, biyo bayan hatsaniyar da aka samu tsakanin yan Hisbah da wasu matasa a unguwar Sabongari dake birnin a ranar Talata.

Ya kuma bukaci matasan jihar da su guji jefa jihar cikin matsalar rikici.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, hukumomin tsaro, da masu fada aji a jihar zasu hada hannu domin ganin cewa an tabbatar da bin doka da oda a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: