Gwamna Bala Mohammed ya nemi hadin kan sarakunan gargajiya wajen yaki da matsalar tsaro

0 71

A Jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su mara wa gwamnati baya wajen yaki da matsalar tsaro da kuma ci gaban al’umma.

Gwamnan ya yi wannan kira ne lokacin da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman, da tawagarsa suka kai masa gaisuwar Sallah a fadar gwamnatin jihar.

Da yake jawabi a madadin Gwamnan, Mataimakin Gwamna Auwal Jatau ya jaddada muhimmancin rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a cikin al’umma.

Ya yi nuni da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan bindiga a yankin Bula, da ke iyaka da Jihar Filato, yana mai bukatar hadin gwiwa domin magance su.

Gwamnan ya bukaci sarakuna da su wayar da kan jama’a kan bukatar kasancewa masu lura tare da bayar da hadin kai ga hukumomin tsaro don dakile miyagun ayyuka.

A nasa martanin, Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman, ya tabbatar da cikakken goyon bayan masarautarsa ga kokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.

Leave a Reply