Gwamnatin jihar jigawa, ta sha alwashin baiwa kowanne daga cikin almajiran da aka dawo mata dasu kudi naira dubu 10,000, tare da kayan sawa, a yayin da suke barin sansanin masu hidimtawa kasa, inda aka killacesu.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abba Zakar, shi ne ya bayyana hakan, da yake ganawa da yan jaridu, kan sakamakon gwajin yaran 16 daga cikin 45 da ya nuna suna dauke da cutar Corona.
Tuni dai guda 29 daga cikinsu, wadanda gwajin ya nuna basa dauke da cutar, suka rabauta da tasu 10,000 da kuma sutura.
Kimanin mutum 44 ne hukumar NCDC ta bayar da rahoton sun kamu da cutar a jihar, a jiya Juma’a, wanda ya kawo jimillar masu dauke da ita 85, sai mutum 2 da suka kwanta dama.
A don haka gwamnatin jihar ta nemi karin goyon baya daga al’umma, a yaki da bazuwar cutar, musamman ta hanyar kiyaye dokokin da aka gindaya, na zaman gida, nisantar juna da kuma ywaita tsafta.