Gwamna Badaru ya sa ranar zaɓen ƙananan hukumomi a Jigawa

0 502

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Jigawa, JISIEC ta tsayar da 29 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ƙananan hukumomi 27 dake jihar.

Shugaban JISIEC, Muhammad Ahmad ya sanar da hakan a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Dutse yau Laraba.

Ya ce an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba don gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin mai zuwa.“Mun yi dukkan shirye-shiryen da suka zama wajibi na ɗaukar ma’aikatan wucin gadi, tsaro, kayan aikin zaɓe, shirye-shirye da sauran abubuwa don tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen yadda ya kamata.

“Za mu tabbatar da cewa mun yi dukkan abubuwa da suka zama wajibi don samun zaɓe na adalci, kuma mai tsafta.“A nan nake yin watsi da jita-jitar da wasu mutane ke yaɗawa cewa ba za a yi zaɓen ƙananan hukumomi ba.

“Ina mai tabbatar wa dukkan wanda ya cancanci kaɗa ƙuri’a a Jigawa cewa tabbas za a yi zaɓe”, in ji shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: