Gwamna Badaru ya halarci bikin ƙaddamar da tsarin Noma don Matasa

0 422

Shugaban ƙasa Muhammadu Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wani sabon tsari Noma don Matasa wanda hukumar NALDA ta shirya domin sanyawa matasa sha’awar harkar Noma.

Shugaba Buhari ya ce har yanzu fannin Noma shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin Nijeriya, saboda fannin ne mafi girma a wajen bayar da gudunmawar haɓakar cigaban GDP.

Tsarin ana sanya rai zai sanyawa matasan Nijeriya masu karatu matakin Digiri ko marasa karatu sha’awar shiga a dama da su don rage yawan marasa aikin yi da kuma cigaba tattalin arzikin ƙasa.

Gwamnan na Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar na tare da takwarorinsa na Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da kuma Yobe Mai Mala Buni duk sun halarci bikin budewar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: